Dokar hana zanga-zanga na aiki a Kaduna har yan zu, ayi hattara – Rundunar ‘yan sanda

0

Jami’in harka da jama’a na rundunar ‘yan sandar jihar Kaduna Muktar Aliyu ya yi shelar cewa har yanzu dokar hana gudanar da zanga–zanga da tattakiya kowace iri na aiki a jihar.

Ya sanar da haka ne a yau Talata da yake zantawa da manema labarai a Kaduna inda ya kara da cewa rundunar ‘yan sanda a shirye take ta hukunta duk wanda ya bijire wa wannan doka.

Aliyu ya yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da gudanar harko kin su batare da fargaba ba cewa gwamnati ta sa matakan tsaro a ko-ina a jihar.

Ya kuma yi kira ga mutane da su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai sannan su kai karan duk abin da basu amince da shi ba ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.

Share.

game da Author