Sanatar da aka ‘falla wa mari’ ta yi magana

0

Sanata Biodun Olujimi ta musanta cewa ta umarci daya daga cikin hadimin ta ya mari wani ma’aikacin majalisar tarayya.

Labarin marin da kuma ramuwar marin da aka yi a kan kumatun ta, ya karade kafafen yada labarai tun jiya Litinin, cewa ta sa an mari wani ma’aikacin majalisar tarayya, shi kuma ya rama marin akan fuskanta a cikin ‘lift.’

Sai dai kuma a lokacin da aka ce an yi mare-maren, dukkan bangarorin biyu ba su iya amincewa sun yi magana da PREMIUM TIMES ba, sai daga baya ne bayan an buga labarin shi ne sanatar ta maida martanin cewa ba ta sa a yi mari ba, kuma ba a mare ta ba,

“Ina sanar da daukacin jama’a cewa na je taro, har na shiga, sai kuma na tuna akwai wani taro a hawa na sama. Sai na shiga na’urar daukar jama’a. To a ciki akwai har da jami’in tsaro na, wanda ke kakkare mutane daga matsowa kusa da ni.

“A hakan ne kuma wani ya shigo ya na ta surfa zagin cewa ana kare waccan.” Haka sanatar ta shaida wa wasu ‘yan jarida.

“Daga nan kuma wasu har da mace suka shigo su na ture shi, su na cewa shi wa ne, ya fita mana. Ni kuma sai na fito na ce abin da ake yi ba daidai ba ne.

Da aka tambaye ta ko ta sa an mari wancan mutumin? Sai ta ce, yaya za ta sa a mari wani. An fito da shi, ni kuma na ce ya tafi, tunda dai ya san bai yi daidai ba.

‘’Ni ban sa a mari kowa ba, domin sau da yawa ma idan na ga mutane a tsaye, na kan ce su shigo wadda na shiga mana ta kai mu sama ko ta sauko da mu kasa.

“Amma ta ya zan sa a mari wani a wannan shekarun nawa? Ai ba hali na ba ne.”

Share.

game da Author