WAYE ZAI KOMA PDP: Saraki da Kwankwaso ne kan gaba a zaben jin ra’ayoyin jama’a na PREMIUM TIMES

0

‘Yan Najeriya da dama da suka bayyana ra’ayoyi su a zaben Jin ra’ayoyin masu karatu kan wani dan siyasa ne cikin jerin wadanda jaridar PREMIUM TIMES ta zayyano zai bi sahun tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar zuwa jam’iyyar PDP daga APC sun biyar.

A zaben dai fiye da mutane 700 sun kada cewa shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki ne ka iya komawa PDP cikin jerin wadanda muka lissafo da suka hada da Danjuma Goje, Aliyu Wammako, Bukola Saraki, Aisha Alhassan, Rabiu Kwankwaso da Rotimi Amaechi.

Kaso mafi rinjaye ya nuna cewa Bukola Saraki mutane suka fi yi wa hasashen zai koma PDP bayan Atiku.

Daga shi sai tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso da mutane 652 suka zaba.

Mutane 559 sun ce Aisha Al-Hassan zata koma PDP, Inda ta zo uku a jerin.

Tsohon Gwamnan Sokoto, Aliyu Magatakarda Wamakko, ya samu mutane 83. Rotimi Amaechi ya samu mutane 244, shi Kuma Danjuma Goje mutane 175 ne suke ganin zai koma PDP.

Share.

game da Author