Honarabul Gudaji Kazaure ya karyata rahotanni da wasu kafafen yada labarai suka yi ta yadawa cewa wai ya soki shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kakkausar murya kan wasu shirye shirye da gwamnatin sa ta kirkiro domin mutanen Najeriya.
Honarabul Gudaji Kazaure, na wakiltar Kazaure/ Roni/Gwiwa/da ‘Yan kwashi ne a majalisar Wakilai.
Da ya ke zantawa da wakilin PREMIUM TIMES a Abuja, Honarabul Kazaure ya karyata wadannan rahotanni yana mai cewa bai fadi haka ba kamar yadda akayi ta yadawa.
” Irin wadannan gidajen jaridu basu da kwarewa sannan ya kamata su dunga tantance abin da za su sanar wa mutane.
” Ko da wasa ban fadi abubuwan da suka rika yadawa ba wai na fadi. Ina Kira ga irin wadannan gidajen jaridu da su mai da hankali wajen tabbatar da inganci, da sahihancin labaran su kafin su yada ta.
Daga karshe ya yabi shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kan kokarin farfado da tattalin arzikin Kasa da gwamnatin sa ke yi da kokarin samar da tsaro da aka mai da hankali a kai.