HIJAB: Ba za mu bari ana yi wa musulunci cin fuska a kasar nan ba – NSCIA

0

Kungiyar koli na addinin musulunci ta yi suka da kakkausar murya da kira ga gwamnati da tayi maza-maza ta sa baki a maganar daliba Firdausi Amosa da makaranta koyar aikin alkalanci ta ki dauka saboda ta sanya hijabi.

Sakataren Kungiyar, Farfesa Salisu Shehu da ya sa hannu a wata doguwar takarda da Kungiyar ta fitar, ya bayyana cewa rashin sanin ya kamata ne da neman ta da zaune tsaye kawai makarantar ke neman yi.

Kungiyar ta ce lallai ta ba makarantar kwanaki domin ta duba wannan bahaguwar shawara da ta yi sannan tana kira ga ma’aikatan Shari’a da ta gaggauta sa baki akan haka ko Kuma a fito zanga-zanga.

” Duk wanda yake ganin zai taka musulunci a kasar nan ya kwana da Shirin
cewa hakar sa bazai cimma ruwa ba domin sai inda karfin mu ya kare.

” Babu wanda zai tsaya a madadin Firdausi a gaban Allah ranar kiyama, saboda haka dole ta bi dokokin da Allah ya umurce ta da bi.

” Ko a kasar Amurka da ake koyi da ita a ci gaba, duk da haka alkalai mata musulmai na iya sa hijabi idan za su shiga Kotu.”

Daga karshe Kungiyar ta gargadi masu yi wa musulunci katsa landan a al’amuran ta da su dai na haka in ba haka ba kuwa za su dandana kudar su.

Share.

game da Author