Tsohon gwamnan jihar Taraba na rikon kwarya Sani Danladi ya canza sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a jihar.
Danladi ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa a yau Talata ne zai canza shekar a mazabar sa na Bachama.
Bayan haka kuma ya shaida cewa babu wanda yake rike da shi a zuciya sai dai ana iya samun rashin jituwa a siyasance.
Danladi ya rasa kujeran sa na sanata ne bayan kotun koli ta kore shi da ga majalisar a wata hukunci da ta yanke a kwanankin baya.
Discussion about this post