Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa wasu daga cikin dalilan da ya sa ya dada Kara samu lafiya sune yadda ya maida hankali sosai wajen bin dokokin likitocin sa.
Buhari ya ce tunda yake bai taba yin ciwo irin wanda yayi ba amma kuma cikin ikon Allah sai gashi Allah ya bashi Lafiya har ya dawo.
” Ina zaton yanzu shekaru na 74 ne amma aka tunasheni cewa 75 ne saboda yadda abubuwan suka kasance.
Buhari ya ce ciwon da yayi ciwo ce ta jarabta da ga Allah, domin bai taba ciwon da ya jijjigashi irin wannan ba.
Ya ce ko a lokacin yakin basasa da suka fafata da sojojin Biafra da fadi tashi a gonakin doya da rogo da suka yi bai ga irin haka ba amma kuma gashi Yanzu ya mika.