Adam Zango – Adam Zango na daga cikin Jaruman da suka shanawa a farfajiyar Finafinan Hausa, a shekarar 2017. Bayan irin rawar ganin da ya taka a finafinan daya fito a shekarar 2017, Adamu ya yi matukar burgewa a wajen rera wakoki da rawa.
A wajen rashin samun yadda ake so ma, Adamu a shekarar 2017, ya fito sau da yawa yana kuka da yadda wasu ke yi masa zagon kasa a harkar sa. Ya lashi takobin mai da wa duk wanda ya nemi ya taka shi martini.
Bayan haka kuma a dan kwanakin nan Adamu ya roki masu karatu da su dai na gyara masa turancin sa idan yayi rubutu a shafin san a Instagram. Cewa ana yi masa haka ne don a tozar ta shi.
Daga nan kuma Adamu ya karrama wasu daga cikin zababbun masoyan sa inda ya yi ganawar cin abinci da su sannan kuma ya bude su kyautuka.
Daga karshe Adamu ya kamala fim dinsa na gwaska da yafi kowa ce fim da aka taba yi a farfajiyar Kannywood tsada.
Adamu ya ce ya kashe sama da Miliyan 12 a shirya wannan fim da zai fito ranar 1 gawatan Janairun 2018.
Rahama Sadau – Idan dai kana maganar yin sharhi ne a Kannywood, to babu shakka sai sunan Rahama Sadau ya fito a koina, Rahama Jaruma ce da tauraruwar ta ke shanawa a farfajiyar finafinai, ba hausa ba har da na turanci.
Idan dai za ayi mata adalci, Ba a taba jaruma ‘yar Arewa da ta burge ba a finafinan kudu, sannan ta goga kirji da jarumai da ake ji da su a kudun Najeriya. Rahama na daga cikin yan wasan da suka samu damar ficewa kasar nan sannan manyan juruman duniya su karbi bakuntan su kamar su shahararran mawakinnan mai suna Akon. Ma abuciya hira da gidajen jaridun duniya ce.
Rahama ta shiga matsaloli da hada da korar ta daga farfajiyar finafinan Hausa na Kannywood, sai dai kuma a shekarar nan, Rahama ta roki gafara sannan ta ci gaba da shiya finafinai da sauransu.
Ummah Shehu – A shekarar 2017, Ba a bar Ummah Shehu a baya ba. Bayan cukukkuye wa da tayi a cecekucen ku ta san addinin ta ko a’a, Ummah a 2017 ta shirya fim dinta na kanta mai suna Burin so. Ummah ta shiga tsaka mai wuya inda mutane sukayi ta jifar ta da maganganu wai bata san addinin ta ba bayan hira da tayi da Momo a talabijin din Arewa.
Tuni dai ta wanke kanta inda a yanzu haka ita ma ta shiga sahun masu shirya finafinai sannan kuma gata jaruma, tayi fim da turanci, tayi da Hausa sannan gashi ta fara shirya wa.
Ali Nuhu – Shi Ali Nuhu, wanda aka fi sani da sarki baya bukatar doguwar bayani a kansa. Ali Nuhu shine baya goya marayu. A 2017 Ali ya taka rawar gani sosai a farfajiyar finafinan Hausa. Ali Nuhu na daga cikin wadanda suka sake tafiya kasar Britaniya a wannan shekara domin karbar kyauta na gwanaye da akaye duk shekara a Kasar Britaniya.
Sadiq Sani Sadiq – Gambo kanin tagwaye. Idan dai shiri na bukatar kwarewa da barkwanci, ka nemi Sadiq. A 2017 Sadiq yayi abin gani. Daga wasu shiri da basu kai ga zuwa fitowa ba kamar su dan Iya, Gimbiya sailuba da sauransu, Sadiq ya nuna bajintar sa matuka.
Nafeesat Abdullahi – Nafeesat, Aminiya , salaha, kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa. A shekarar 2017 Nafeesat ta dawo daga hutun ta sannan ta kom harkar fim gadan gada. Idan dai ana maganar saka hoto ne a Instagram to Nafeesat ta daga tuta wannan shekarar sannan fim din ta na Fatima ko Zara ya burge. Wata da ta kalli fim din ta kara wa ‘yar ta suna Nafeesat don kauna.
Fati Washa – Fati Washa na daga cikin yan wasan da suka shana a wannan shekara. Akwai manyan finafinai da aka tallata su a wannan shekara inda wasunsu ma har sun fito. A bayanin da muka samu Fati na daga cikin wadanda aka fi saka su a finafinan 2017. Ta fito a fim din Gwaska return da wasu fina finai da dama.
Maryam Yahaya – Maryam Yahaya itace Karama amma kuma mai gallaza wa manya azaba. Idan baka gane ba kalli fim din Mijin Yarinya. Duk da dai sabuwar fitowa ce a harkar finafinai ta na shanawa a farfajiyar finafinan Hausa.
Discussion about this post