Wani mazaunin garin Biu ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sai da ya kirga gawa 22 a kasuwar Biu bayan harin kunar bakin wake da wasu mata biyu suka Kai a kasuwar yau.
‘Yan matan dake dauke da jigidar bama-bamaisun shigo kasuwar ne kamar sun zo siyayya ashe wannan bala’i zasu aikata.
Daya ta tada nata bam dinne a wurin masu sai da waya, dayan Kuma a wajen ‘yan kaji.
An Kai mutane Sama da 50 da suka Sami rauni a sanadiyyar harin asibiti a Biu.
Ko da yake rundunar ‘yan sandan jihar Barno sun ce mutane 13 ne suka rasa su a harin.
Discussion about this post