Tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar ya sanar da komawa tsohuwar jam’iyyar sa, PDP.
Atiku ya bayyana haka ne yau a shafin sa na Facebook inda ya Kara da cewa sun warware duk wata sabani dake tsakanin sa da da jam’iyyar PDP.
Idan ba’a manta ba, Atiku ya fice daga jam’iyyar APC a makon da ya gabata ne cewa yadda gwamnatin APC din ke mulki ba abin da ‘yan Najeriya ke bukata bane.
Yayi ikirarin doke Buhari idan yayi takara da shi a 2019.
Discussion about this post