Ko Buhari ya amince yayi Takara a 2019 ko mu maka shi a kotu – Ganduje

1

Gwamnnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya fadi cewa a shirye suke da su maka shugaban kasa Muhammadu Buhari a Kotu idan yace ba zai yi takara a karo na biyu ba.

Ganduje ya bayyana haka ne bayan ganawar da jam’iyyar APC reshen jihar Kano tayi inda ta tsayar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takaranta a zaben 2019.

Wadanda suka halarci taron sun hada da duka shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar da mataimakan su, ‘yan majalisar jihar 34 da wasu jiga-jigan jam’iyyar a Kano.

Kakakin fadar shugaban Kasa Garba Shehu ya ce Buhari ya ji su amma bai ce Eh ba bai ce A’a ba.

Gwamnan jihar Jigawa Mohammed Badaru ya halarci taron.

Share.

game da Author