SABON SALO: Za ayi wa sojoji 403 ritaya cikin sati mai zuwa

0

Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa cikin mako mai zuwa za a yi bikin yi wa sojoji 403 ritaya.

A ta bakin Kwamandan Cibiyar Koya Wa Sojoji Sana’o’in Hannu, Austine Jatau, ya ce za ayi bukin ne domin a ranar ce za a yaye su daga koyon sana’o’in hannun da suka yi kwas a cibiyar tasa.

Air Vice Marshal Jatau ya ce an koya musu sana’o’in hannu ne domin idan suka yi ritaya, su dogara da kan su a rayuwar da za su ci gaba da kasancewa a ciki.

Jatau ya ce daga cikin sojojin 403 da ritayar ta shafa, 281 sojojin kasa ne, sai sojojin ruwa 17 da kuma sojojin sama 105.

Za a yi bikin yaye su daga cibiyar koyon sana’o’in tare kuma da yi musu ritaya a ranar 15 ga Disamba, 2017

Share.

game da Author