Masu garkuwa sun yi garkuwa da tsohon ministan wasanni Damishi Sango a hanyar sa na zuwa Abuja daga garin Jos.
Iyalan Sango sun shaida wa jami’an ‘yan sanda cewa an sace Sango da misalin karfe 2 na rana ne a hanyar sa na zuwa Abuja domin shirin gangamin jam’iyyar PDP da za a yi ranar Asabar.
Masu garkuwan suna neman miliyan 100 kafin su saki Damishi Sango.