Shugaba Muhammadu Buhari ya kara wa’adin dukkan Manyan Hafsoshin Tsaron Kasar nan.
Kakakin Ministan Tsaro, Kanar Tukur Gusau, ya tabbatar da haka daga bakin Ministan, Mansur Muhammad Dan-Ali.
Manyan Hafsoshin da aka yi wa karin wa’adin sun hada da: Janar Abayomi Gabriel Olonisakin, wanda shi ne Babban Hafsan Tsaro na Kasa, sai Laftanar Janar Tukur Buratai, Babban Hafsan Askarawan Kasa, sai kuma Vice Admiral Ibok-Etelkwe Ibas, Babban Hafsan Sojojin Ruwa da Air Marshal Sadique Baba Abubakar, Babban Hafsan Mayakan Sama.
An ce an kara musu wa’adin ne saboda kokarin su na ganin an kakkabe Boko Haram a kasar nan da kuma himmar su wajen shawo kan matsalar tsaro a kasa baki daya.
Sanarwar ta ce wannan wa’adi da aka kara musu, ya yi daidai da abinda dokar kasa ta 1999 ta shimfida.