Akalla mutane uku ne suka rasa rayukan su a rikicin garin Bwari dake babban birnin Tarayyar Najeriya, Abuja.
Ministan Abuja, Muhammed Bello ya ce dalilin wannan rikici dole asa dokar hana walwala a garin har sai an sami dawowar zaman Lafiya.
Rikici ya barke da safiyar Litinin a garin Bwari in da sanadiyyar haka akan babbake babbar kasuwar Bwari din.
Wasu ‘yan kabilar Gbayi me sun ka kai wa Hausawa harin ramuwar kan zargin kashe wani dan kabilar Gbagyi da suka ce wai Hausawa ne suka aikata.
Wani mazaunin garin Bwari ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa a dan kwanaki biyun nan ana zaman doya da manja tsakanin ‘yan kabilar Gbayi da Hausawa mazauna garin Bwari.
Gbagyi na zargin Hausawa da kashe wani dan uwan su bayan an tsinci gawar sa a garin da safiyar litinin din nan.
” Hakan bai yi musu dadi ba inda waken daukar fansa sai rikici ya kaure har ya Kai ga kone Kasuwar Bwari din.
Jami’an tsaro na ‘yan sanda da sojoji sun isa garin Bwari sannan an kakkafa shinge a mashiga garin.
Discussion about this post