Rikici da ya barke da safiyar yau Litinin ya bar kasuwar Bwari a babbake bayan wasu ‘yan kabilar Gbayi sun kai wa Hausawa harin ramuwar gaiya kan zargin kashe wani dan kabilar Gbagyi da suka ce wai Hausawa ne suka yi.
Wani mazaunin garin Bwari ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa a dan kwanaki biyun nan ana zaman doya da manja tsakanin ‘yan kabilar Gbayi da Hausawa mazauna garin Bwari.
Gbagyi na zargin Hausawa da kashe wani dan uwan su bayan an tsinci gawar sa a garin da safiyar litinin din nan.
” Hakan bai yi musu dadi ba inda waken daukar fansa sai rikici ya kaure har ya Kai ga kone Kasuwar Bwari din.
Jami’an tsaro na ‘yan sanda da sojoji sun isa garin Bwari sannan an kakkafa shinge a mashiga garin.