TSAKANIN KEMI DA GWARZO: Rashin Biyayya ne ko Laifi ya yi? Ainihin dalilin da ya sa aka dakatar da Gwarzo

0

Jiya Laraba ne Ministar Harkokin Kudi, Kemi Adeosun ta dakatar da Babban Daraktan Hukumar Kula da Hada-hadar Kudade, SEC, Munir Gwarzo.

Ba Gwarzo ne kadai aka dakatar a hukumar ba. Dakatarwar ta hada da Shugaban Fannin Sadarwar kafafen yada labarai, Abdulsalam Habu, da kuma Anastasia Braimoh, wadda ita ce shugabar sashen bada shawarwarin da suka jibinci harkar shari’a a hukumar.

Dakatarwar da aka yi wa su Gwarzo ta biyo bayan zargin da aka ce ministar na yi masa na bai wa kan sa kudaden sallama har naira miliyan 104.8.

Akwai kuma wani zargi da ake yi masa cewa ya na amfani da wani kamfani, wanda shi ne daraktan kamfanin, mai suna Medusa Investment Ltd., wanda ya ke bai wa kwangiloli masu dimbin yawa.

Sai dai kuma wata kwakkwarar majiya ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa, bayan tiya, akwai wata caca, domin an dakatar da Gwarzo ne don yaki yarda ya bada kai borin Minista Adeosun ya hau.

Majiyar ta ce an yi wani taron sirri ne tsakanin Ministar da Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Kudi da kuma Gwarzo. A wurin taron, majiyar mu ta ce ba a tattauna komai ba sai batun kamfanin mai na Oando.

An ce Kemi ta nemi Gwarzo da ya dakatar da binciken da ya ke yi wa Oando.

Tun da farko dai Gwarzo a matsayin san a Shugaban SEC, ya gano cewa akwai wata harkalla da Oando suke yi na lissafin adadin hada-hadar su ta shekara.

Yayin da Kemi ta nemi ya daina binckien, majiya ta ce Gwarzo ya shaida mata cewa bai yiwuwa a daina bincken, domin idan aka daina, to kima da darajar SEC za ta zube a idon ‘yan Najeriya, kuma za a dora musu alamar tambayar cewa akwai wani abu a kasa kenan.

Kwakkwarar majiya ta ce Kemi ta yi masa barazanar ko dai ya daina bincikar Oando, ko kuma ta dakatar da shi, sannan ta yi binciken wata harkalla da shi Gwarzon aka ce wai ya tafka a baya.

“A kan me Minista Kemi za ta ce Gwarzo yayi harkalla can baya? Watanni goma fa da bullar batun harkallar, kuma tuni EFCC da ICPC sun bincikin harkallar, ba a ga wata ill aba.

“Kudin da aka ce Gwarzo ya arce da su, kudi ne da doka ta ce ya karba idan yagama Kwaminshinan da ya rike a hukumar kafin ya zama shuagaban ta baki daya.

Majiyar ta ci gaba da cewa, “me ya sa Kemi za ta kafa kwamiti bayan tuni EFCC da ICPC duk sun bincike shi?

Share.

game da Author