Anyi kira ga hukumar Inshorar Lafiya ‘NHIS’ ta saka cutar Daji a shirin ta

0

Shugaban hukumar inshorar kiwon lafiya na kasa, NHIS Attahiru Ibrahim ya ce da yiwuwar saka masu fama da cutar daji a karkashin shirin hukumar.

Ya fadi haka da yake ganawa da wata kungiya mai zaman kanta ‘Project Pink Blue’ a ofishin sa dake Abuja.

Kungiyar ta kai ziyara ofishin NHIS ne don yin kira ga hukumar da ta sa daukar nauyin kula da masu fama da cutar daji musamman yadda kula da cutar ke da tsada a shirin ta na inshorar lafiya.

Ibrahim ya ce matsalar rashin kudi da hukumar ke fama da shi ne ya hana su shigar da masu fama da cutar cikin shiri.

“Hukumar a shekarar 2014 ta dauki nauyin kulawa da masu fama da cutar daji da suka kai 100 amma saboda rashin kudi ya hana mu ci gaba da shirin.”

Share.

game da Author