Sanata ya sa sojoji sun fizgo Dan Majalisa daga helikwafta

0

Sanata da Dan Majalisar Tarayya sun kai ruwa rana a filin jirgin saman Yola, abin da ya kai ga har jami’an sojoji suka fizgo dan majalisar daga cikin helikwafta.

Wannan abin kunya ya faru ne a ranar Laraba lokacin da suka hadu a filin jirgin domin daukar su a helikwafta zuwa wurin rabon kayan agaji ga al’ummar da Boko Haram ta tarwatsa.

Sanata Abdul’aziz Nyako da ke wakiltar Adamawa ta Tsakiya da mamba mai wakiltar kananan hukumomin Michika da Madagali, Adamu Kamale, sun kusa ba hammata iska a cikin helikwafta, yayin da ake kusa da tashi sama.

An dai shirya zuwa Madagali ne domin kai kayan agaji wadanda NEMA za ta raba, tare da rakiyar masu ruwa da tsaki a harkar.

PREMIUM TIMES ta samu labari ta hannun wani jami’in tsaron da aka yi rikicin a gaban sa cewa ‘yan majalisar guda biyu duk sun ci mutuncin junan su a bainar jama’a.

“Da farko dai an shirya cewa helikwafta zai dauki wasu masu ruwa da tsaki zuwa inda za a raba kayan agajin a ranar Laraba. An zo wurin shiga jirgi ne sai aka ga Sanata Nyako na cewa bai kamata Hon. Kamale ya shiga tare da su a jirgin ba, saboda shi Nyako shi ne Shugaban Kwamitin Rabon Kayan Agaji.

Yadda Nyako ya sa sojoji suka kekketa min riga a cikin jirgi-Hon. Kamale

“Sakamakon mummunan harin bam da Boko Haram suka kai a Madagali, sai Gwamnan Jihar Adamawa da sauran manyan jihar suka roki gwamnatin tarayya ta kawo daukin taimakon agaji daga NEMA.

“A matsayi na ma Dan Majalisa mai wakiltar garin da harin bam din ya shafa, ni ne na shiga na fita muka tsara yadda za a kai wadannan kayan agaji, kuma shi ma Sanata Nyako din a matsayin sa na Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira da kuma Hukumar Agajin Gaggawa, NEMA. Sai NEMA ta wakilta Hafsan Sojojin Sama, Ohemu ya sa-ido kan yadda za a raba kayan.

“To sai Rundunar Sojojin Sama ta ware wani helikwafta da zai dauke mu zuwa inda za a yi rabon kayan agajin, a ranar Laraba. Ina cikin tawagar tafiyar da Sanata Nyako da Ohermu da sauran wasu.

“Amma abin takaici, yayin da nake shirin hawa jirgin, Sai Sanata Nyako ya bada umarnin kada a bar ni na shiga ciki, saboda shi wai shi ne Shaugaban Kwamitin Rabon Kayan Agaji, kuma shugaban tawaga.

“Duk wani kokari da na yi domin na ja hankulan Sanata Nyako da Ohemin ya ci tura. Daga nan kawai sai babban jami’in sojojin sama din nan ya sa yaran sa su ka fizge ni, suka kekkyeta min riga, sannan suka kulle ni a gadirum. Fizga ta da sojoji suka yi na gurje kuma na kwalje jiki na sanadiyyar yadda suka fincike ni daga cikin jirgi, suka yi kasa da ni.

Ya kara da cewa, “an sha kai hare-hare a Madagali, an lalata garin an gallaza wa al’ummar garin amma Sanata Abdul’aziz Nyako baita ba zuwa ko da jaje sau daya ba.

Ban sa an ci mutuncin sa ba-Sanata Nyako

Sanata Abdul’Aziz Nyako ya musanta cewa ya ci mutuncin Hon.

“A makon da ya gabata na je ofishin Hukumar NEMA domin duba ayyuka a matsayi nan a shugaban kwamiti kan NEMA DA IDP. Sai suka nemi na jagoranci kai kayan agaji a garuruwan Gulak da Madagali. Suka tabbatar min cewa za su sama min helikwafta, sannan suka ce na ba su sunayen wadanda za su kasance su ne masu rakiya ta.

“Ni na bayar da sunayen mambobin kwamitin nan a Majalisar Dattawa. Sai kuma aka shaida min cewa NEMA ta ce Babban Daraktan NEMA ya ce a fada min Sanata Binta Garba, wacce ke wakiltar yankin za ta je ita ma. Sai na kara da sunan ta da na Shugaban Majalisar Tarayya mai kula sa IDP da NEMA, Hon. Jibrin Galjumari.

“To abin haushi, bayan mun gama hawa cikin helikwafta, har an tayar da jirgin ana shirin tashi, sai kawai muka ga Kamale ya afko cikin jirgin. Wannan babban ganganci da kasada ce yi.

“Ai ya ma gode Allah da ya sa ya na da sauran kwana a gaba, maimakon ya yi ta zargi na. Mun cika da mamaki a lokacin da aka ce mana ai dan majalisar wakilai ne.

Shi ma kodinatan NEMA na Arewa maso Gabas, Bashir Garga, ya dora laifin a kan Kamale, wanda ya ce kadan kyas ya rage da Kamale ya sheka barzahu.

”Duk wadanda za su yi tafiyar sai da aka ba mu sunayen su, kuma sunan Kumale ba ya ciki.” Inji Daraktan.

Share.

game da Author