Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, Abuja ta shigar da kara babban kotun tarayya dake Abuja tana neman a yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa saboda kashe mijin ta Bilyaminu Bello Halliru da tayi.
Ana zargin Maryam Sanda da daba wa mijin ta Bilyaminu fasasshen kwalba da niyyar kashe shi.
Bayan aikata haka, Bilyaminu ya rasu sanadiyyar wannan sara.
‘Yan sanda sun ce wannan abu ya faru ne a gidan su da ke unguwan Wuse, Zone 2 ba Maitama ba kamar yadda ake ta yadawa.
Ba a tsayar da ranar fara sauraron karar ba, sai dai har yanzu Maryam na tsare a hannun ‘yan sandan.