Majalisar Dinkin Duniya za ta gina wa ‘yan gudun hijira gidaje 288

0

Majalisar Dinkin Duniya ta fara aikin gina gidaje 288 ga ‘yan gudun hijira a jihar Barno, kamar yadda kamfanin dillanci labarai ya ruwaito.
Rahoton dai y ace wadanda za su ci moriyar gidajen su ne wadanda Boko Haram ya tarwatsa, ya raba su da muhallin su.

Hukumar ta ce ana nan ana ci gaba dai ginin gidajen 288, amma akwai sauran 12 da za a gina, su cika 300, wadanda ba a fara aikin gina su ba tukunna.

An rigaya har An kammala gina karamin asibitin ganin likita, rumfunan kasuwa 288, shaguna 20 da kuma ginin makaranta daya mai ajujuwa 6 da kuma dakin ajiye kayan makaranta.

Rahoton ya ce Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ce za ta wadata asibitin da magungunan da suka kamata.
Hukumar ta kuma raba buhunan takin zamani 210, maganin kashe kwarin shuka 105 da kuma awakai 120 da wasu kayan noma da dama ga manoman yankin.

Ta kuma kara da cewa nan gaba za ta gina wa al’ummar yankin ofishin ‘yan sanda, rijiyar burtsatse, na’urar hasken sola ga asibitin da kuma raba wa masu kiwon kifi kayan dabarun kiwon kifi domin a inganta rayuwar al’ummar.

Sannan kuma za ta bai wa matan karkarar da su da ‘yan mata wani tallafi da kuma koya musu dabarun sana’o’in hannu da kananan kasuwanci tare da bai wa jami’an kananan hukumomi horo.

Share.

game da Author