Majalisar Tarayya za ta amince da dokar kafa hukumar NCDC a Disamba

0

Shugaban kwamitin kiwon lafiya a matakin farko da hana yaduwar cutuka na majalisar dattijai Mao Ohuabunawa ya ce majalisar tarayya za ta amince da dokar da zai bada damar kafa hukumar kula da hana yaduwar cutuka na kasa NCDC kafin karshen wannan shekarar.

Ya ce majalisar a shirye ta ke don ganin ci gaban fannin kiwon lafiya a kasar nan musamman fannin hana yaduwar cutuka.

Ya kuma ce majalisar za ta hada hannu da hukumar NCDC, hukumar NACA da hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko don ganin gwamnati ta ware kashi 1 na kudade da take samu duk shekara wa fannin Kiwon lafiya

Share.

game da Author