YOYON FITSARI: Za ayi wa mata aiki kyauta a asibitocin gwamnati

0

Gwamnatin tarayya ta sanar cewa duk manyan asibitocin dake mallakin ta za ta yi wa mata da ke fama da cutar yoyon fitsari aiki kyauta.

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewale ya sanar da hakan inda ya kara da cewa gwamnati ta hada hannu da wata kungiya mai zaman kanta ‘Engender Health/Fistula Care Plus’ don ganin hakan ya yiwu sannan kungiyar ta dauki nauyin samar da kayan aikin da duk asibitocin za su bukata.

Share.

game da Author