Hukumar hana yaduwar cutar kanjamau ta kasa NACA ta bayyana cewa kashi daya bisa hudu na mutanen da ke dauke da cutar kanjamau ne ke samun magani a Najeriya.
Shugaban hukumar Sani Aliyu ya sanar da haka inda ya kara da cewa mutane miliyan uku ne a kasan ke dauke da cutar kanjamu wanda ke bukatar akalla Naira 50,000 don samun magani amma a yanzu haka miliyan daya ne kawai ke samun magani.
” A lissafe hukumar na bukatar naira biliyan 150 don samar wa kashi 60 bisa 100 na mutanen da ke dauke da cutar a kasar nan.”
Ya ce a yanzu haka jihohi 9 ne kawai a ke iya samar wa rabin mutanen da ke dauke da cutar magani.
Sakamakon haka ya sa hukumar ke kira ga gwamnatin tarayya da ta kara ware isassun kudi don kula da masu dauke da cutar.
Discussion about this post