KANJAMAU: Za a tallafa wa Najeriya da Dala miliyan 100

0

UNAIDS ta bada tallafin dala miliyan 100 don yin bincike akan rage yaduwar cutar kanjamau a Najeriya daga shekarar 2018.

Jami’in hukumar Erasmus Morah ya ce UNAIDS ta yi haka ne don taya gwamantin tarayya yaki da cutar kanjamau da ta ke yi ganin bincike ya nuna cewa miliyan 3.2 na mutanen Najeriya na dauke da cutar.

Ya kuma ce gwamantin kasar Amurka ce za ta bada mafi tsoka a cikin tallafin sannan asussun majalisar dinkin duniya kan kawar da kanjamau, tarin huka da zazzabin cizon sauro za ta bada sauran.

Share.

game da Author