TARIN FUKA: Najeriya na cikin kasashe 7 dake fama da cutar

0

Duk da tallafin da Najeriya ke samu daga kasashen duniya, ta na daya daga cikin kasashe 7 dake fama da cutar tarin fuka a duniya.

Bisa ga binciken da hukumar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO ta gudanar kan cutar a shekaran 2017, Najeriya na matsayi na shida cikin jerin kasashen in da akwai mutane miliyan 10.4 dake dauke da cutar sannan kashi 10 bisa 100 daga cikin su na dauke da cutar kanjamau Kuma.

Binciken ya nuna cewa cikin kashi 10 bisa 100 din dake dauke da cutar kanjamu da tarin fuka, kashi 6.3 ne kadai ke da masaniya kan cutar da suke dauke da shi.

Binciken ya kara nuna cewa babbar matsalar dake sa ana samun kara yaduwar cututtukan a Najeriya shine rashin gano cutar da wuri da rashin ingantattun magungunan da za su yi aiki akan cututtukan da basa jin magani.

Sauran kasashen duniyan dake fama da irin wadannan cututtuka sun hada da India, Pakistan,Indonesia, Sin,Philippines da Afrika ta kudu.

Share.

game da Author