Danyen Mai ya yi tashin gwauron zabi

0

Shekaru biyu kenan rabon da danyen Mai yayi irin tashin da yayi safiyar litinin din yau.

Yau dai danyen mai ya Kai Dala 62.44 kowace ganga.

Hakan dai zai yi wa kasashen kamar su Najeriya dadi ganin yadda suke bukatar kudaden shiga domin gudanar da ayyukan ci gaba a Kasar.

Sannan Kuma hakan ya na da nasaba ne kuwa dalilin kame da yarima Muhammad bin Salman na Kasar saudiyya yayi na wasu attajiran Kasar da wasu ‘yan gidan sarautar kasar da aka kama da hannu dumudumu wajen yin sama da Fadi da kudaden kamfanonin da suke shugaban ta.

Cikin sauye-sauyen da yake kokarin yi a kasar, za a shigo da kamfanin Mai na kasar Aramco domin yin Kasuwa cin Mai a
Kasar.

Share.

game da Author