El-Rufa’I ya ziyarci ‘yan majalisan dake wakiltar Kaduna a majalisar Tarayya

0

A yau Laraba ne gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rura’I ya kai ziyara ta musamman ga ‘yan majalisar tarayya dake wakiltar jihar don ganawa da su kamar yadda ya saba a duk dan wani lokaci don neman goyon bayan su kan himman da gwamnatin sa ta sa a gaba na gyara fannin ilimin jihar.

Ya ce tun da ya hau mulkin jihar yake kokarin gyara fannin ilimi ta hanyar gyara ajujuwa da gina sabbi, canza darussan da ake koyarwa, gyara albashin malamai da sauran su.

” Kada mu manta cewa kusan dukkan mu mun yi karatu ne a makarantun gwamnati inda yanz muka amfani dashi wajen daga kafadar mu sama da yin tunkaho a matsayin da muke yanzu.”

” Idan haka ne me zai hana mu samar da irin wannan ilimin da mu ka samu ga ‘ya’yan mu ta hanyar musanya dakikan malamai da kwararru a makarantun gwamnatin jihar.?”

“Ina tabbatar muku da cewa baza mu tauye hakkin malaman da za mu musanya ba. Za mu biya kowa albashin sa da duk wani alawus da ya kamata mu bashi.”

Dan majalisa Yakubu Barde na majlisar wakilai, wanda shine ya jagoranci wadanda suka zauna da gwamnan a wannnan ziyara ya tabbatar wa gwamnan cewa za su bashi goyan bayan da yake nema domin ganin ya cimma burin sa na gyara makarantun gwamnati na jihar.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne El-Rufa’I ya bada umurnin gwada kwarewar malaman jihar ta hanyar gudanar da jarabawa a kansu.

Sakamakon jarabawar ya nuna cewa kashi 66 bisa 100 na malaman da suka rubuta wannan jarabawa ba su ci makin da ake buka ta ba.

Dalilin haka ne yasa gwamnati ta yanke shawarar musanya dakikan malaman da sabbi da aka tabbatar da kwarewar su don koyar da yara a makarantun jihar.

A yanzu hakan jihar Kaduna ta sanar cewa tana bukatan malamai 25,000 sannan ta karbi wasikun neman aikin mutane 43,806.

Share.

game da Author