Idan abin ya gagara zamu tattara namu-inamu mu kuma kasar Kamaru – Mazauna Madagali

0

Mazauna garuruwan karamar hukumar Madagali jihar Adamawa sun koka cewa idan har gwamnati ba za ta iya samar musu da da zaman lafiya na dindindin ba to za su koma kasar Kamaru da zama .

Mutanen sun fadi haka ne da su ke ganawa da sanatocin da suka ziyarce su tare da jami’an hukumar bada agajin gaggawa NEMA a garin Madagali.

Shugaban karamar hukumar Madagali, Yusuf Muhammad, ya ce ba agajin abinci da kaya suke bukata ba yanzu.

” Mu fa yanzu ba agajin abinci da kaya bane ya dame mu. Kawo mana karshen wannan hare-hare ne ya fi damun mutanen wannan karamar hukuma, wanda idan abin ya gagara zamu tattara namu-inamu mu koma kasar Kamaru da zama.”

Yace duk da fama da hare-hare da muke yi a wannan yanki, anyi banza da su kamar ba yan kasa Najeriya, sannan ya roki gwamnati da ta kara jibge jami’an tsaro a kauyukan karamar hukumar don samar da tsaro ga mutanen jihar.

Sanata Binta Koji ta yaba wa shugaban karamar hukumar na karfi hali da yayi da nuna jarumta wajen fadi wa gwamnati gaskiya.

Tace lallai abinn da ya fadi gaskiya ne kuma dole a duba hakan don mutanen jihar.

” Kananan hukumomin Michika da Madagali, basa more komai daga gwamnati. Abin da ke damu na shine wani irin laifi ne muka yi wa gwamnati take mana haka.” Inji Binta Garba.

Shugaban kwamitin bada agajin gaggawa na majalisar dattijai, Sanata AbdulAziz Nyako ya ce ya yi matukar farin ciki da yadda suka fito suka fadi gaskiyar abin da ke damun su, kuma zai isar wa majalisa kukan mutanen yankin.

Share.

game da Author