Buhari, Amurka da Kungiyar Amnesty sun yi tir da harin Mubi

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Kasar Amurka da Kungiyar Afuwa ta Duniya, Amnesty International sun yi tir da harin da aka kai a wani masallaci a garin Mubi, Jihar Adamawa, inda akalla mutane 50 suka rasa rayukan su, wasu da dama suka jikkata.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ce ta bada wannan sanarwa, ta hannun jami’in yada labaran ta, Heather Nauert, wanda ya bayyana harin a matsayin tsatsar ta’addanci.

Amurka ta kuma aika da ta’aziyya ga daukacin ‘yan Najeriya da kuma iyalin wadanda aka kashe.

“An bi wadanda su ka rasa rayukan na su har cikin masallaci inda suke ibada aka karkashe su. Wannan ya nuna irin rashin tausayin da ‘yan ta’adda ke da shi, wanda kawai su dai su tada hankulan ‘yan Najeriya ne muradin su.

“Irin wannan rashin imani da Boko Haram ke nunawa wajen kashe jama’a, na kara kaimi da kwarin-guiwar taimakawa mu kawar da wannan barazana ta hanayar hada karfi da Najeirya da sauran kasashen yankin.

‎Ita ma Amnesty International ta yi Allah wadai da harin.

Daraktan kungiyar a Najeriya, Osai Ojigbo, ya ce, “Wannan hari ya na nuna har yau Boko Haram basu gaji da kisan al’umma ba. Alhakin wadanda suka rasa rayukan su duk ya na a wuyan Boko Haram, musammam abin takaicin da suke yi na amfani da yara suna kai harin-kunar-bakin-wake.

Tun da farko dai Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tir da wannan mummunan hari, tare da umartar a kara jibge jama’an tsaro a yankin.

Ya nuna rashin jin dadin sa ga wannan hari.

Shi ma gwamnan jihar Adamawa, Jibiralla Bindow, baya ga fasa halartar taron Majalisar Zartaswa a Abuja da ya yi, ya kuma kafa kwamitin bincike da zai gano musabbabin rikicin da ya barke tsakanin Fulani da wasu kabilun jihar.

Share.

game da Author