Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC ya ce jam’iyyar APC bata yanke shawarar tsayar da Buhari dan takaran shugaban kasa a inuwar jam’iyyar ba.
” Kamar yadda kowa ya sani bamu tsayar da Buhari dan takaran jam’iyyar mu ba. Sannan a sani muna da doka a jam’iyyar mu wanda ya zayyana yadda za a gudanar da zabe da tsayar da dan takara.”
” Babu wani gwamnan da zai fito ya ce ya tsayar da Buhari dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC. Buhari mutum ne mai so abi doka, kuma jam’iyyar mu na da doka, ita za mu bi. Idan ma har muka yadda mu tsayar dashi a matsayin zabin jam’iyya, Ina ganin bamu kauce ma dokar jam’iyya ba sannan bamu saba wa dokar hukumar zabe ba.”
Tinubu ya ce idan ba a manta ba gwamnan jihar Ondo Akeredulu na daga cikin wadanda sukayi wa buhari aiki sannan kuma suka zabe shi a zaben fidda gwani a 2015.
Bayanan da yayi a taron kungiyar kabilar Yarbawa Afenifere da akayi a jihar Ondo, Tinubu ya kara jaddadawa ‘yan kabilar yarbawa cewa za suyi kokarin ganin an ci gaba da samun hadin kan yan kabilar da samar musu ababen more rayuwa.