Wasu sanatoci yau sun koka kan yadda ake tafiyar da gwamnati a kasar nan, ganin yadda kowa ke yin abin da ya ga dama ba tare da an taka masa birki.
Wannan cece-kuce ya rikita majalisar na dan wani lokaci, bayan Sanata Dino Melaye ya jawo hankalin majalisar kan yadda nuna ikon mulki da hukumomin tsaron kasar nan suke yi wa junan su musamman kan abin da ya auku tsakanin jami’an hukumar tsaro na sirri, SSS da jami’an hukumar EFCC a wata samame da suka kai gidajen Tsohon shugaban NIA, Ayo Oke a gdan sa da ke unguwar Matama, Abuja.
EFCC dai ta kai sameme ne a gidajen tsoffin shugabannin SSS da NIA, domin su kama su. Amma sai dakarun da ke tsaron su suka hana jami’an ko kusantar gdajen su. Hakan dai ya tada hankulan mutane mazauna yankin da masu harkoki a unguwar.
Da yake tofa albarkacin bakin sa sanata Biodun Olujimi ya ce dole a ankarar da shugaban kasa kan irin wadannan abubuwa dake faruwa domin hakan na nuna kamar babu mai iko ne akan su da abi da ke faruwa.
” Yanzu kowa na yin abin da ya ga dama kamar babu wani mai iko akan shi. Hakan yana sa aga kamar gwamnatin ma ba ta san inda ta dosa ba.”
Fadin haka ke da wuya, shugaban masu rinjaye na majalisar, Ahmed Lawan ya kwabi sanata Olujimi da ya iya wa bakin sa domin cewa da yayi kamar babu shugaba mai cikakken iko a kasa. Ya ce fadin hakan na nuna kamar an bar kasar ne babu fada aji.
” Ko da Buhari zai tafi ganin likitocin sa a kasar Britaniya, ya mika wa mataimakin sa mulkin kasar, sai yanzu kwartsam wani ya fito ya ce babu shugaba, ba dai dai bane.
Daga karshe majalisar ta ce za ta kafa wata kwamiti domin binciken yawan yamutsi da ake samu tsakanin jami’an tsaron kasar nan.”
Discussion about this post