ABIN DA MASU KARATU SUKA CE: Kashi 60 bisa 100 sun ce El-Rufai ya musanya wadanda suka fadi jarabawa amma a horas da wadanda basu ci ba

0

Sakin wasu daga cikin takardun  amsoshin da malaman firamaren Kaduna suka ba da a jarabawar gwaji da akayi ya tona musu asiri.

Mafi yawa daga cikin mutane na yi wa shirin ganin neman tozarta malaman ne kafin a saki wannan takardun amsoshin malaman.

Dalilin haka ne muka nemi ji daga bakin masu karanta mu domin jin ra’ayinsu kan  shirin musanya wadanda suka fadi da kwararru a shafin mu na facebook.

Akalla mutane sama da 600 ne suka fadi ra’ayinsu kan wannan shiri na gwamnati.

Kashi 60 bisa 100 na mutane sun nuna cewa a musanya malamai da kwararru shine ya fi cancanta sai dai kuma sun ba da shawarar a horas da wadanda basu ci bane ko kuma a sama musu abin yi.

Kashi 30 kuma sun ce zalunci ne koran malaman. Abar su su ci gaba da karantar da yaran makarantar haka in da kasha 15 bisa 100 suka ce sun a tareda duk yadda gwamna yake so.

A Horas da malamai amma kada a koresu.

Bala Garba Idris Wannan wata shiryaryiyace kawai amma a horar dasu asabar da lahadi a tabbatar da kwarewarsu suci gaba da aikinsu ko a sallamesu ta hanyar ritaya amma ba koraba.

Muhammad Danbarno A Matsayina Na Dan Jahar Kano Kuma Malamin Makaranta Kamata Yayi Ai Koyi Da Jahar Kano Ma’ana A Kyalesu Amma A Turasu Makarantun Horon Malamai (colleges Of Education,N T I) Musamman Na Ranakun Asabar Da Lahadi(part Time)

Nura Aliyu Gaskiya abinda ya kamata ayi shine a dauki tsarin da akabi a Kano baa Kori kowaba lokacin engineer RABIU Musa kwankwaso. Malaman zasu dunga karatunsu a week end, dakuma duka working days Bayan hutu Na tsawon shekaru 3 har su samu shedar NCE.

Yusuf G Balewa Yakamata gwamnatin Kaduna ta tura Malaman da suka fadi jarabawan in service sai a debo sabin kwararrun malamai sucigaba da koyarwa kafin wanda sukaje nemo karin ilimi su dawo,kafin sudawo kuma gwamnati ta kara bude wasu sabbin makarantu kunga za’a samu isassun malamai kuma babu wanda aka kuntata masa. Wanda kuma bazai iya zuwa neman karin ilimi ba sai yayi ritaya,wanda kuma baifito da sakamako mai kyau ba sai gwamnati ta sauya masa wajen aiki,duk dalilin hakan shine kada a kuntatawa wani ko toshe masa hanyan cin abincin sa. Allah yasa mudace Ameen.

Muhammad Adamu Muhammad Ra ayina shine yaturasu su karo karatu suna koyarwar kamar yadda DR. RABIU MUSA KWANKWASO YAYI AJIHAR KANO wannan itace mafuta iharza ayi masu adalci

A Musanya malamai

Abubakar Ashraf In dai kyautatawa zaa yi a canza musu wasu ayyukan koda masu karancin albashi ne,sai a dauki kwararrun in akayi haka kowa ya samu sauki, da su marasa kwarewar da kuma Alumma da gwamnatin ita kanta

Dahiru Musa Duk wanda baice jarabawaba acenza masa wurin aiki, kamar yadda naga sakamakon wasu malaman gaskiya abinkunyane ace malaman makarantane su

Ahamed Sani Abdullahi Indai mal nasiru yana yine don talakawar jihar kaduna toh kamata yayi ya kyale malaman nan da aikinsu amman ya dauki wasu sabbi. su kuma ya basu daman qara krt ai daman malaman sunyi karanci a makarantu

Anas Abdulwahab Ae ko shakka babu,a masanya su kawai da kwararrun tunda su basu cancanta ba

Gwamna ya yi dai dai.

Ummun Afrah Garga Duk wanda yace hakan da akayi ba akautaba yaran shi basu makarantai gwamnati ko kuma shibayi makarantan gwamnati ba.don duk wanda yasan makaranta gwamnati yasan me malaman abinda sukeyi shike biyan su ba iyayan yaraba zaibiya su kudi abanzane malami sai yafi wata bai shiga class ba don ALLAH aganin ku in an biya malamin nan meyaci bayan baiyi aikin shiba

shaka Usman Wali Kawai a koresu saboda yawancin su basuyi karatuba alfarmace takaisu ga wannan matsayin sannan idan baa koresuba to taya dalibanda suke koyarwa zasu yi karatu mai kyau shiyasa aka tserema arewa ta bangaren karatun Boko zakaga malami bai san komaiba kuma wai shine Mai koyarwa don haka nake kira ga gwamnatin kaduna tayi gaggawar kaorarsu tasa wadanda suka kware.

Saminu A Yaro Gobirawa Daidaine a musanya malaman dasuka fadi da kwararrru aa baza’a barsuba sbd ilimi zaikuma baya tunda basuganiba taya zasuganar dawasu adaiyi abunda yadace da su busuye daidaiba dakira zuwaga yajinaiki a kada arufi makarantu akanhakan adai dauki wasu yafi dacewa yanzu daya dagacekinku da akwai yaransa ceki shema dayaci akurisu

Share.

game da Author