Gwamantin tarayya ta karyata korafe korafen da asibitocin dake kula da wanda maciji ya sara a jihohin Gombe da Filato na rashin maganin warkar da saran.
Idan ba a manta ba kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa asibitoci a jihohin Gombe da Filato sun koka kan rashin maganin saran maciji da suke fama da Shi wanda sanadiyyar haka ya sa mutane 250 suka rasa rayukan su a cikin watanni uku.
Asibitocin da suke fama da wannan rashin sun hada da babbar asibitin Kaltungo, Ali Mega Pharmacy, duk a Gombe da Comprehensive Medical Centre, Zamko,a Filato.
Ma’aikatan asibitocin sun ce dalilin haka ne ya sa sukan sa wa mara lafiya ne Ido ‘har sai Allah ya dauki abin sa’.
Sai dai Kuma da jin haka sai kwamishinan kiwon lafiya na jihar Filato, Kuden Kamshak a hira da PREMIUM TIMES ya karyata wannan korafi na wai babu maganin saran maciji a Kasar nan.
” Sai dai mutane su koka kan rashin kudin siyan maganin a asibitin amma ba rashin sa.”
Ya kuma karyata cewa da aka yi wai babu maganin a asibitin Pankshin.
Daga karshe ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ce akwai isassu maganin saran maciji a kasar nan wanda aka siyo tun bara.
Ya kuma ce gwamanti na kokarin ganin an fara yin irin wannan magani a kasar nan domin samun sa cikin sauki.