KASAFIN 2018: Najeriya ta kara yin watsi da alkawarin da ta dauka kan kiwon lafiya

1

Najeriya na ci gaba da yin kwan-gaba-kwan-baya tare da yin tafiyar-kura, inda a wannan shekarar ma ta kara yin watsi da alkawarin da ta daukar wa Kungiyar Hada Kan Kasashen Afrika tun shekaru 16 da suka gabata, inda ta sha alwashin fifita bangaren kiwon lafiya domin kula da ‘yan kasar ta.

Cikin 2001, Najeriya ta dauki nauyin taron kungiyar a Abuja, inda shugabannin Afrika suka sha alwashin bayar da kashi 15 bisa 100 na kasafin su wajen inganta kiwon lafiya.

Tun bayan wancan kudiri da suka daukar wa alkawari, har yau Najeriya ba ta taba kashe sama da kaso 6 bisa 100 na kasafin ta a bangaren kiwon lafiya ba, ballantana har ta kai kashi 15 bisa 100 da ta yi alkawari.

Mafi yawa da aka taba kashewa shi ne 5.95 a cikin 2012, inda aka ware wa bangaren kiwon lafiya wannan adadi.

Sai dai kuma wani abin mamaki shi ne, yadda a wannan kasafi na 2018 da gwamnati Buhari ta yi, Naira Bilyan 340 kacal za a kashe wa bangaren kiwon lafiya, wato kashi 3.9 ma kenan daga cikin naira tiriliyan 8.6 da aka kasafta za a kashe a wannan shekara mai zuwa.

Idan za a iya tunawa, kasafin na bangaren kiwon lafiya na 2018, bai ma kai na 2017 ba, wanda shi kashi 4.6 ne, haka ma bai kai na 2016 ba, wanda shi kuma 4.23 ne.

Share.

game da Author