” A ra’ayi na ban ga dalilin kafa Hukumar raya yankin Arewa maso Gabas ba” – Kabiru Marafa

0

A yau Laraba wasu ‘yan majalisan dattijai suka nuna rashin amincewar su da kafa sabuwar hukumar raya yankin arewa maso gabacin kasar nan wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a kafa a makon da ta gabata.

Sanatocin sun kushe kafa hukumar ne saboda zame wasu jihohi da suke ganin ya kamata ace suna cikin jihohin da dake cikin wannan hukuma cewa suma sun yi fama da hare-haren Boko Haram.

Shugaban masu rinjaye na majalisar sanata Ahmed Lawal da shine ya jagoranci mahawaran a zauren majalisar ya mika godiyar sa da kafa wannan hukuma ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Bayan haka ne sanata Kabiru Marafa na jam’iyyar APC ya ce a ra’ayin sa bai ga amfanin kafa hukumar raya yankin arewa maso gabas ba domin a ganin sa kowace sashe a kasar nan na bukatar irin wannan kula da hukuma idan har aka ce wai za a duba irin haka.

” Ina daya daga cikin kadan din da suka ki amincewa da kafa wannan hukuma tun farko domin ba haka ya kamata a yi ba. Maimakon kirkiro da irin wannan hukumar, da wani shiri ne akayi domin samar wa wadanda suke jikkata da kuma rasa dukiyoyin su sanadiyyar ayyukan Boko Haram a wadannan yanki da zai samar musu da ababen more rayuwa da musanya musu abubuwan da suka rasa amma ba a kafa hukuma na dindindin da zai sa a yi amfani da makudan kudade wajen gudanar da ayyukan ta ba.”

Ya kuma kara da cewa dalilin kin amincewa da kafa hukumar shine ganin yadda aka zare wasu jihohi kamar Kano da Filato hara da Babban birnin tarayya da aiyukkan Boko Haram ta shafa a cikin jihohin da za su more ayyukan wannan hukumar.

Shi kuwa sanata Ben Bruce na jam’iyyar PDP ya ce ” Kafa hukumomi irin wadannan zai lashe kudade masu yawa domin dole sai an gina ofisoshin da ma’aikata za su yi aiki a ciki wanda hakan ya sa nake tunani ko nayi kuskure wajen zaben da nayi na amincewa da kudirin a baya.”

“Ina ganin zai fi kyau idan aka baiwa gwamnatin jihohin yankunan da irin haka ya auku dasu nauyin raya wuraren maimakon amincewa da kafa hukumar da muka yi.”

Daga karshe sanatocin sun yanke shawaran jira zuwa lokacin da dokar kafa hukumar za ta bukaci gyara sai su tsara yadda sauran jihohin da aiyukkan Boko Haram ta shafa yadda za su amfana da irin wanna shiri.

Share.

game da Author