Yadda ‘Yan Sandan Najeriya su ka azabtar da mu, su ka kwace mana kudi, har lalata su ke yi da matan aure

0

Duk da cewa a naba su horo a kan yin kaffa-kaffa da hakkin jama’a da ’yancin dan adam, amma ‘yan sandan Najeriya na ci gaba da kulle jama’a ba bisa ka’ida ba, azabtar da su da kuma cin zarafin su. Haka wasu da su ka dandana kudar rashin imanin ‘yan sanda su ka shaida wa kwamitin binciken take ‘yancin jama’a a Legas.

Kwamitin binciken wanda ya kunshi mambobi daga Hukumar Kula da Yancin Dan Adam, ta yi zaman ta a kan binciken take hakkin jama’a da ’yan sanda ke yi, a Najeriya ranar Litinin.

Kungiyoyi da hukumomi sama da 30 ne su ka halarci zaman sauraren koke-koken da jama’a su ka rika gabatarwa.

Sanarwar bayan taron da aka fitar ta yi kira ga kungiyoyin sa-kai da su rika dora dukkan alhakin take hakkin dan Adam a wuyan DPO Da ke yankin da abin ya faru.

Idan dai ba a manta ba, cikin 2014, wasu kungiyoyin sa-kai na kare hakkin jama’a sun yi hadin guiwa da Rundunar ‘Yan sandan Najeriya domin fito da manhajar horas da ‘yan sanda, wadda za ta maye gurbin tsohon tsarin horon da ake ba su.

Tsohuwar manhajar dai babu batun kula da hakkin jama’a a cikin ta, abin da shi ne sabuwar manhaja ta yi kokarin samarwa daidai gwargwadon yadda ake kiyaye wancan hakki ko ‘yanci a kasashen duniya.

Sai dai kuma duk da karbar wannan sabuwar manhaja da Rundunar ‘Yansandan Nijeriya ta yi, hakan bai hana su ci gaba da azabatarwa, gallazawa da kuma cin zarafin jama’a ba. Abin ya kai su har ga kisan jama’a ba tare da an hukunta ba.

SHAIDUN IRIN AZABTARWAR DA ’YAN SANDA KE YI

Wasu mutane shida da suka dandana kudar azabtarwar ‘yan sanda, sun bayyana wa kwamitin sauraren koke-koken irin azabtarwar da ‘yan sanda su ke musu:

Sylvester Ihejirika, matashi ne mai shekaru 27, ya bada labarin yadda ya sayo wata mota samfurin Toyota Sienna, kirar 1999 daga hannun wani dillalin motoci a Fatakwal. A cinikin ya ce an biyo shi naira dubu goma, amma da ya kasa biya da wuri, sai aka hada shi da ‘yan sanda.

An tsare shi a ofishin ‘yan sanda na Olusegun Obasanjo da ke Fatakwal. Daga nan aka rika daukar sa daga wannan gari zuwa wannan ya na shafe kwanaki a hannun ‘yan sanda.

Ihejirika ya ce an lakada masa dukan tsiya, an ci mutuncin sa, sannan kuma an karbi tsabar kudi har naira dubu 170,000 a hannun iyalan sa, wadanda aka biya ta hanyar yin taransifa daga asusun ajiya a banki na wani jami’in dan sanda da aka sani da suna Scorpion.

Daga nan sai ya gabatar da shaidar takardar shigar da kudi bankin ajiyar Scorpion.

Shi yanzu abin da Ihejirika ken ema, shi ne a sakar masa motar sa, sannan kuma ‘yan sanda su biya shi kudin sa naira dubu 170,000.00.

Shi ma Paul Nwachukwu, wanda aka daure tare da Ihejirika, ya tabbatar da labarin irin azabtarwar da ‘yan sanda suka yi masa a Abeokuta, musammman irin yadda wani azababben dan sanda mai suna Scorpion.

Ita kuwa wata mata mai suna Blessing Nwachukwu, ta shaida yadda ta na shekara 43 lokacin ta na aiki a karkashin wani kamfani, inda mai kamfani ya sa ‘yan sanda su ka kama ta a bisa zargin sa wai ita ce ta dauke masa Dala dubu 50,000.

Ta ce an fara tsare ta a ofishin ‘yan san a Ikoyi, daga baya aka dauke ta aka maida ta shashen hana satar mutane a ofishin ‘yan sanda da ke Panti, Yaba.

Ta ce ta na tsare an rika karbo kudade daga dangin su, tun daga kan ta har kan sarauran matan da ke tsare. Ba haka abin ya tsaya ba, sai da ‘yan sanda su ka yi lalata da kanwar ta da kuma matar wani da ke tsare a ofishin ‘yan sandan.

PREMIUM TIMES ta gano cewa wannan abin takaici ne har ta kai ga Kwamishinan ‘yan sanda ya shiga maganar bayan da ‘yan jarida su ka rika yayata maganar, sai ya ce a yi bincike.

Abin takaici inji ta, tun da aka kammala bincike, har yau ba a fitar da abin da suka binciko ba. Sauran masu korafi sun ci gaba da gabatar da koke-koken su.

A karshe kwamitin ya umarci Hukumar Kare ‘yancin dan adam da ta gaggautaq shiga maganar kuma ta taimaka musu wajen gano ‘yan sandan da aka yi ikirarin cewa sun yi aika-aikar. An kuma ce kowa zai nuna ‘yan sandan da su ka ci zarafin su, kuma a gaggauta gufanar da su domin kotu ta hukunta su.

-Gambu mai wakar barayi ya ce;

“Ba sata mai ban-takaici,

’Yan sanda ke sata mai ban-takaici,

In kah hwadi da mota kam mace can,

In dai dangi ba su na kusa,

In dai ’yan sanda na rigan su,

Ba ishe ko sisi ake ba,

Sai a damre cikin banza da wohi,

Mi aka wa wata tada-kura!”

Share.

game da Author