Na yi matukar farinciki da kafa Hukumar kula da yankin Arewa Maso Gabas – Aisha Buhari

0

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari tana taya mutane da gwamnatocin yankin arewa maso gabas murnan kafa hukumar raya yankin arewa maso gabas NEDC.

Maitaimaka wa Aisha kan harkokin yada labarai Suleiman Haruna ya sanar da haka a Abuja inda ya kara da cewa Aisha ta ce kafa hukumar da aka yi zai taimaka wajen share hawayen mutanen yankin da suka yi ta fama da ayyukan Boko Haram.

Aisha Buhari ta ce kafa wannan hukumar ya dade a ranta wanda kafa shi zai kawo babbar ci gaba ga mutanen yankin.

Daga karshe Aisha Buhari ta yi kira ga wadanda nauyin tafiyar da hukumar ya rataya a kan su da su yi kokarin ganin kukumar ta sami nasara wajen share wa mutanen yankin hawaye.

Aisha Buhari na daga cikin wadan da suka matsa don ganin an kafa wannan hukuma.

Share.

game da Author