Motoci na ba kyautar Sufeton ‘Yan sanda bane – Inji Aisha Buhari

0

Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta karyata ikirarin da Sanata Hamma Misau ya yi cewa Sufeto Janar na ‘yan sanda Ibrahim Idris ya saya mata motoci biyu na kece raini, samfurin SUV.

Aisha ta maida wannan martani ne a shafin ta na Twitter, inda ta rubuta cewa, “Da motoci biyu da na ke da su na ke amfani.” Sai dai kuma ta sha suka da caccaka a shafin na ta, daga masu maida mata martani, kasancewa ba ta rubuta cewa ta amshi motocin ko kuma ba ta amsa daga Sufeto Janar din ba.

Sanata Misau, daga jihar Bauchi ya jefa Aisha Buhari a cikin jangwangwamar da ke tsakanin sa da Sufeto Janar Idirs, inda manyan biyu su ke ta sabule wa junan su zani a kasuwa.

Share.

game da Author