Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON, Abdullahi Mohammed, ya bayyana cewa Mahukuntan kasar Saudiyya sun bada sanarwar cewa za su rufe rajistar adadin maniyyatan da zu yi aikin Hajji na shekara mai zuwa a watan Mayu.
Muhammad ya yi wannan jawabi ne a jiya Alhamis yayin da ya ke ganawa da Shugabannin Hukumomin Jin Dadin Alhazai na jihohin kasar nan, a Abuja.
Ya ce bada wa’adin na daya daga cikin sabbin tsare-tsare da gwamnatin Saudiyya ta shigo da su domin tabbatar da an yi aikin Hajjin 2018 an kammala lami lafiya.
Shugaban na Hukumar Alhazai ta Kasa, ya kuma shawarci jihohi da su tabbatar da sun fara shiri tun yanzu, domin tabbatar da cewa sun cika sharuddan da kasar Saudiyya ta gindaya, kafin wa’adin ya cika.
Ya kuma ja kunnen su da su kakkabe duk wani cin hanci da danniya da harkallar da ake yi a lokacin rajistar biya kudaden aikin Hajji.
Ya kuma jinjina wa shugabannin hukumomin Alhazai na jihohi dangane da rawar da kiwanen su ya taka wajen ganin an samu nasarar da aka samu a yayin aikin Hajjin bana da ya gudana, a 2017.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa shugabanni 16 ne daga jihohi tare da shugabannin shiyya su ka samu halartar taron.