Iyalin tsohon shugaban kwamitin fansho, Abdulrasheed Maina, sun tabbatar da cewa jami’an SSS sun taimaka wajen shigo da Maina kasar nan a asirce, tare da ba shi kariya a duk inda ya ke.
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda jami’an tsaro karkashin Lawan Daura su ka yi wa shigar-burtu zuwa cikin kasar nan tare da ajiye shi a wani gida da jama’a ba su san inda ya ke boye ba.
Maina ya kasance a boye tun bayan da PREMIUM TIMES ta fallasa labarin maida shi aiki da kuma shigo da shi a asirce.
Sai dai kuma duk da cewa an cire shi daga aiki, kamar yadda Shugaba Buhari ya gaggauta bayar da umarni, Buhari bai ce komai dangane da rahoton da Shugabar Ma’aikata ta tura masa dangane da yadda aka maida Maina kan aikin sa a asirce ba.
Wani dan’uwan Maina, mai suna Aliyu Maina ne ya bayyana irin rawar da SSS su ka taka wajen shigo da Maina, bayan arcewar da ya yi daga kasar nan tun cikin 2013. Su dai SSS an fi sanin su da DSS.
“Gwamnati ce ta nemi Abdulrashid ya dawo ya taimaka mata domin a tsarkake hanyar tara kudaden haraji tare da toshe duk wata kofar da manyan kuraye ke watanda da kudaden gwamnati.” Haka jaridar Daily Trust ta ruwaito Aliyu Maina ya bayyana jiya a Kaduna.
“A haka ya amsa rokon wannan gwamnati ya dawo cikin kasar nan. Kuma tuni ya na aiki tare da jami’an tsaro na DSS wadanda su ne ke ba shi kariya.”
PREMIUM TIMES ta binciko cewa tuni kafin shugabancin Lawan Daura, DSS na tare da Maina, domin a lokacin gwamnatin Jonathan, jami’an sun dura naira milyan 152 a cikin wani asusun kamfanin bogi mallakar Maina da ke a bankin Fedility.