Kotu ta saki dan Atiku

0

Kotu a jihar Legas da ta yanke hukuncin a tsare dan tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar a dakin ajiye firsinoni ta sake shi, sai dai da sharadin zai dawo wa Fatimo, tsohuwar matar sa ‘ya’yan su.

An tsare Aminu ne a yau Laraba, bayan yanke hukuncin ayi haka da kotun Majistare da ke unguwar Tinubu, a Legas.

An tuhumi Aminu da bijire wa umarnin da mai shari’a Kikelomo Ayeye ta ba shi a ranar 11 Ga Oktoba, 2017, da ya gabatar da dan sa da ya dauke daga tsohuwar matar sa Fatimo Bolori.

A ranar 11 Ga Oktoba ce alkali Ayeye ya umarce shi da ya gabatar da yaron mai suna Amir mai shekaru shida, yau Laraba a kotu domin a fara sauraren karar da ke tsakanin sa da matar sa Fatimo da suka rabu tun 2011.

Share.

game da Author