Ana zaton yaduwar cutar ‘Monkey Pox’ a jihohi 11 – Ministan Kiwon Lafiya

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya sanar da cewa akwai yiwuwar yaduwar cutar ‘Monkey Pox’ a jihohi 11 na kasar nan.

Adewole ya ce akwai mutane 74 da ake zaton sun kamu da cutar saai dai ba’a tantance ko iat bace ko zazzabi ne.

Ya sanar da haka ne da yake zantawa da manema labarai a yau Laraba bayan kammala taron samun madafa kan yadda za a kau da cutar bayan zaman majalisar zartaswa na mako-mako da akeyi.

Jihohin da suka kamu da cutar sun hada da Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River, Delta, Ekiti, Enugu, Imo, Lagos, Nasarawa, Rivers da Abuja.

Bayan haka ministan kiwon lafiya ya karyata jita-jitar da ake ta yadawa wai sojoji na kokarin yada cutar ‘Monkey Pox’ a makarantu ta hanyar yi wa yaran makaranta alluran rigakafi.

Ya ce bisa ga dokar kasan rundunar Sojin Najeriya bata da damar bada alluran rigakafi na kowani iri a fadin kasar nan.

‘‘Idan har za a bada alluran rigakafi dole ne ma’aikatan kiwon lafiya ta yi aiki da gwamnatin jihar da za a bada alluran’’.

Share.

game da Author