Mafi yawan lokuta mutane da dama basa maida hankali wajen kula da lafiyar jikin su musamman idan suna dan Jin wani ciwo-ciwo a sashe na jikin.
Wani likita dake asibitin Murtala a Kano, Abdullahi umar ya gargadi mutane da su guji nuna halin ko in-kula da wasu alamu na ciwo da su Kan hi a sassa na jikin su domin yakan iya zama alama ce na ciwo da zai iya yi wa rayuwarsu barazana.
Ya bayana irin wadannan alamu kamar haka:
1. Ciwon kafada na hanun hagu; Yana yiwuwa cutar bugawar zuciya ne ko kuma matsalolin dake tattare da rashin karfin garkuwan jiki.
2. Ciwon kafadan hannun dama; sanadiyyar kamuwa da cutar koda ko kuma samun matsaloli da ke tattare da madacin mutum.
3. Ciwon baya; Yana iya yiwuwa cutar da ke kama kodar mutum wanda ake kira ‘Kidney stones’,buguwa a kashin baya, ciwon baya da sauransu.
4. Ciwon kafa; Yana yiwuwa hardewar jijiyoyin kafa ne ko kuma matsalar daskarewar jini.
5. Ciwon kai mai tsanani; sakamakon kamuwa da cutar shanyewa bangaren jikin mutum ko kuma matsalar daskarewan jini.
6. Ciwon wuya; sakamakon kamuwa da cutar dake kama huhu ko kuma matsalolin da ya Shafiu numfashin mutum.