Hukumar EFCC ta ce Abdulrasheed Maina dai na nan a matsayin mai laifi wadda ta ke nema ruwa a jallo.
Hukumar ta fadi da haka ne bayan fallasa shi da wani rahoton gidan jaridar PREMIUM TIMES tayi cewa Maina dai da yake ta boye- boye, bashi Najeriya bashi Dubai ya dawo har an bi ta bayan fage an sake nada shi mukamin mataimakin babban darekta.
Ko da yake an danganta hakan da saka hannun wasu ministoci da suka hada da ministan Harkokin Cikin Gida Abdulrahman Dambazau da na Shari’a Abubakar Malami.
Dambazau dai a ranar Lahadi ya ce bashi da wata masaniya akan haka cewa a tambayi shugaban ma’aikatan gwamnati wato ‘Head of Service’.
Shima haka kakakin ma’aikatan Shari’a ya ce ba ya zaton minista Malami na da hannu a wannan sarkakiya.
Idan ba a manta ba, an kori Maina a cikin 2013. Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ce ta kore shi, sakamakon wata takardar da Shugaban Ma’aikata na lokacin ya rubuta ya na neman a kore shi, a bisa zargin harkallar biliyoyin kudaden fansho.
Wani darakta a ma’aikatar ya ce bai kamata a dawo da Maina ba, saboda ya na da tuhumar da ake masa a kotu, wadda ya tsallake ya gudu ya bar kasar tun 2013.
“Kuma doka ta haramta a maido da shi har sai kotu ta wanke shi tukunna.”
Cikin 2012 ne dai aka zargi Maina da yin harkalla har ta naira bilyan 100. A cikin 2010 ne gwamnatin Goodluck Jonathan ta nada shi ya tsarkake harkar biyan kudin fansho.
Daga zargin da aka yi masa ne Majalisar Dattawa ta gayyace shi. Daga nan ta umarci a gagauta kama shi. Shi kuma Maina sai ya maka Majalisar Dattawa kotu, tare da Sufeto Janar na ‘Yan sanda na lokacin MD Abubakar, kuma ya shiga wasan buya.
An kai karar su a kotu a ranar 21 Ga Yuli, 2015 tare da Stephen Oronsaye. An caje su da aikata laifuka na harkalla har 24. Sauran sun bayyana a kotu, amma shi Maina ya tsere.
An ce Maina ya shafe shekaru a Dubai, inda daga can ya rika kamun-kafa a cikin gwamnatin Buhari domin a maida shi kan mukamin sa.
Babu inda aka bada sanarwar dawo da Maina kan aiki. Abin ne dai gwamnatin tarayya ta yi a cikin sirri.
Dama kuma a farkon wannan shekarar, an rika buga fastar Maina inda ake nuna ya na neman takarar Gwamnan Borno, amma dai ba a ce ga jam’iyyar da ya ke ciki ba.