A fallasa sunayen berayen har da na gida – Shehu Sani

0

Sanata mai wakiltan Kaduna Ta tsakiya, kwamared Shehu Sani ya yi kira ga gwamnatin tarayya da tabbata ta fallasa sunayen ‘ya’yan jam’iyya mai mulki da aka kama da laifin handame kudaden jama’a.

Shehu Sani ya fadi haka ne a shafin sa na Facebook inda ya kara da cewa kada gwamnati ta tsaya ga ‘yan jam’iyyar adawa ta zayyano har da na su dake mulki.

Kotu ta yanke hukunci cewa lallai gwamnati ta zayyano sunayen wadanda aka kama sun ragargaji kudin gwamnati.

Ta hanyan yin barkwanci Shehu Sani ya danganta su da wasu kungiyoyin kwallon kafa kamar su ‘Paris Saint Germain’ da ‘Dynamo Cabal FC players,”

Share.

game da Author