Jita-jita ce kisan da ake yadawa wai an yi a jihar Zamfara – Rundunar ‘Yan sanda

0

A yau Alhamis rundunar ‘Yan sandar jihar Zamfara ta karyata wata jita-jita da ake ta yadawa a yanar gizo cewa wai makiyaya sun kashe mutane 120 a jihar.

A wata hira da yayi da PREMIUM TIMES kwamishina ya tabbatar wa gidan jaridar cewa hakan bai faru ba a ko ina a jihar sannan ya yi kira ga gidajen jaridu da su tabbatar da ingancin labari kafin su yada ta.

Alkali ya ce bincike ya nuna musu cewa wani Waziri Mohammed ma’aikacin hukumar bada agaji na gaggawa ‘NEMA’ ne ya saka labarin a shafin sa na ‘Facebook’.

Alkali ya ce Mohammed ya ci gaba da cewa irin wannan rikicin bai tsaya ba a yankin arewacin kasan ba kawai.

Wasu cikin abokan Mohammed sun karyata labarin da ya sa a shafin sa na ‘facebook’ in da su ka kalubalance shi da ya fadi inda abin ya faru. Bayan haka Mohammed ya saka hotan kisan da Boko Haram ta yi ne a shekaran 2014 a wata makarantar maza dake jihar Yobe inda yara 59 suka mutu.

Daga karshe Alkali ya yi kira ga mutane da kada su maida hankalinsu akan irin wannan jita-jitar sannan manema labarai da su tabbatar da ingancin labarai kafin su watsa shi.

Share.

game da Author