Wani manomi ya tallafa wa makarantu 10 da littafan rubutu 5,000

0

Wani manomi ya tallafa wa makarantu 10 da littafan rubutu 5,000 a garin Kabba jihar Kogi.

Da yake hira da manema labarai, manomin mai suna Akinwale Malcom ya ce ya yi haka ne don agazawa talakawan dake jihar da zaka ga littafi ma yakan gagare su siya wa ‘ya’yan su.

Ya kuma kara da cewa saboda haka ne ya bude gidauniyya domin tallafawa karatun talkawan yankin.

” A shirye nake da in ci gaba da agaza wa yara ‘yan makaranta musamman ‘ya’yan talakawa domin samun ilimin boko mai amfani.”

Yanzu na kammala shiri don yin irin haka a makarantun da ke garin Bunu da zaran na gama da na yankin Kabba’’.

Iyaye da malaman makarantun da Malcolm ya agaza wa ya sun jinjina masa kan wannan abin alkhairi da yayi wa ‘ya’yan talakawa.

Share.

game da Author