Buhari ya roki Saraki da Dogara kan abin da ya faru a kofar shiga fadar gwamnati

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya roki shugaban majalisar Dattawa da na wakilai da su yi hakuri da abin da ya faru a kofar shiga fadar shugaban Kasa da su da sauran ‘yan majalisan da suka zo fadar tare.

Buhari ya roki shugabannin biyu ne yayin tattaunawa da suka yi a fadar sa.

Jami’an tsaron fadar shugaban Kasa sun hana tawagar shugabannin majalisar biyu shiga fadar shugaban Kasa bayan sun umurce su da su sauko daga motocin su a dauki hotunan su Kuma suka ki.

Duk da cewa shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki da mataimakin sa Ike Ekweremadu da na majalisar wakilai da mataimakin sa an basu damar shiga sun ki shiga saboda hana sauran ‘yan uwan su shiga.

Daga baya sai Saraki da Dogara suka dawo domin amsa gaiyatar shugaban Kasa.

Bayan ganawa da suka yi, Buhari ya ce an daga zaman cin abincin tare da sauran ‘yan majalisar zuwa ranar Talata mai zuwa.

Share.

game da Author