Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattawa ta amince masa ya ciwo bashin Dala biliyan 5.5 daga waje.
Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ne ya Karanto hakan a wata wasika da shugaban kasa ya aika majalisar yau Talata.
Buhari yace za ayi amfani da kudaden ne wajen biyan ayyukan da aka sa a kasafin kudin 2017 sannan kuma a biya wasu basussuka na cikin gida.